Political News 🌐
Trending

Zaben fitar da gwani na APC: Taron APC ya mamaye muhawarar shafukan sada zumunta a Najeriya

Zaben fitar da gwani na APC: Taron APC ya mamaye muhawarar shafukan sada zumunta a Najeriya

  • Zaben fitar da gwani na APC: Taron APC ya mamaye muhawarar shafukan sada zumunta a Najeriya

Ƙarshen tika-tika tik, in ji masu iya magana. Kuma yau ake gobe sai labari.

Dandalin Eagle Square da ke babban birnin Najeriya Abuja ya dauki harama tsaf don zaɓen fitar da gwani na ƴan takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam’iyyar APC.

Sai dai rikici ya cukuikuye jam’iyyar ta APC gaba ɗayanta gabanin taron.

Daga dambarwar rashin tsayar da magana ɗaya a tsakanin gwamnonin jam’iyyar, sai batun cimma matsaya da yin sulhu, lamarin da ya gagara, sai batun ra’ayin shugaban jam’iyya da kuma maganar da shugaban ƙasa ya yi cewa ba shi da ɗan takara.

A yanzu kuma da aka wayi gari a ranar zaɓen sai ga kiraye-kirayen neman shugaban jam’iyyar Abdullahi Adamu ya sauka, biyo bayan rahotannin da ya yi cewa a zabi Shugaban Majalisar dattawa Sanata Ahmed Lawan a zaman dan takarar Shugaban kasa na jam’yyar.

Sai dai da alama a ƙarshe dole wuƙa da nama su koma hannun daliget, waɗanda su ne za su yi zaɓen, don haka ma ake ganin su a amtsayin masu ƙarfin faɗa a ji a wannan gabar.

Ƴan Najeriya dai sun kasa yin shiru kan wannan zaɓe, domin kuwa tuni suka cika shafukan intanet waɗanda su ne manyan kafafen sadarwa a yanzu, inda suke bayyana ra’ayoyinsu.

Yayin da wasu suka mayar da hankulansu wajen tattaunawa a kan rikicin da ya dabaibaye jam’iyyar gabanin zaɓen fitar da gwanin, wasu kuma sun mayar da hankali ne wajen faɗar wanda suke ganin shi ne zai yi nasara a zaɓen.

Abin da ake faɗa a shafukan sada zumunta

A shafin tuwita dubban mutane ne suke tattauna wannan batun, kuma maudu’in #APC Convention na cikin wadanda suka fi tashe.

Unilorin Marlian@TheMarlianya ce: “Ya Ubangiji, a yau mu ƴan Najeriya suna jira mu ga ayoyinKa kan abin da ya shafi zaɓen fitar da gwani na APC. Allah Ka shige mana gaba.

Wani kuma mai suna PeeJee @Sijibaba daliget ya bai wa saƙo inda ya ce: “Ya ku daliget don Allah ku zaɓi mutumin kirki a zɓen fitar da gwanin APC na yau.”

Malomo @baloo1010 ya ce: “Zaɓen fitar da gwanin APC tamkar babban zaɓe. Daga masu faɗa a ji sai maciya amana.”

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button