Political News 🌐
Trending

Zaben fitar da gwani na APC: Labaran ƙarya da aka yaɗa a kansa

Zaben fitar da gwani na APC: Labaran ƙarya da aka yaɗa a kansa

An yi ta yaɗa labaran ƙarya kafin da lokacin da kuma bayan kammala zaɓen fitar da gwani na ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya, a daidai lokacin da ƴan ƙasar suka mayar da hankali kan lamarin da zai zama tamkar shimfiɗa ga zaɓukan watan Fabrairun 2023.

An yaɗa hotuna da bidiyo na ƙarya a shafukan sada zumunta da muhawara.

Batun shirin zaɓar mataimakin ɗan takara Musulmi da Bola Tinubu na APC ke yi a matsayinsa na ɗan takara Musulmi, wanda tuni ya ƙaryata, na daga cikin waɗanda aka yaɗa.

An yaɗa labarin ne a ƙoƙarin kawo ruɗani a tsakanin al’ummar ƙasar da kuma zuzuta bambancin addini.

Bidiyon Atiku da gwamnonin AP

Jim kaɗan bayan sanar da nasarar Bola Tinubu a zaɓen fitar da gwanin APC, an yaɗa wani bidiyo na TikTok a Facebook a wani shafi da aka sa masa suna: Support Nigerian Military.

Bidiyon ya nuna ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar adawa ta PDP Atiku Abubakar da shugaban majalisar dattijai Ahmed Lawan da wasu ƴan APC da kuma gwamnonin APC din a wani falo.

Bidiyon ya nuna kamar suna wata ganawa ce, an jiyo ɗaya daga cikinsu yana cewa da Hausa “Mu koma babban falon”.

An wallafa bidiyon tafe da wani saƙo da ke cewa “Wadannan su ne mutanen da suka zaɓi Bola Tinubu ɗazun nan a zaɓen fitar da gwani, amma cikin ƙasa da awa 24 ga su nan suna tare da ɗan takarar jam’iyyar adawa da zai fafata da shi.”

An wallafa bidiyon fiye da sau 500.

Ikirarin cewa tsananin talauci ya sa mutane na sayar da yatsunsu a Zimbabwe ya ja hankali a Najeriya
Da gaske ƙarfe na maƙalewa a hannun waɗanda aka yi wa riga-kafin korona?
Labaran karya da ake yadawa kan batancin da ake zargin an yi kan Annabi
Bayanai sun nuna cewa wani shafi mai suna Boboske1 ne ya fara ɗora bidiyon a TikTok ranar 23 ga watan Janairun 2022 ba tare da bayani ba.

Sannan kuma a ranar 22 ga watan Janairun 2022 ma Atiku Abubakar ya wallafa hotunan da aka ɗauka a irin wannan yanayin dai.

Kuma tufafin jikinsu duk irin na bidiyon ne sannan a falon da aka ɗauki bidiyon aka yi hotunan.

 

By C.E.O Founder OF Mr ATG News Auwal Telan Gayu

Hello my Fallowers My Name is_Real_Auwal_Telan Gayu_ C.E.O_Founder OF_MR ATG News.com_my followers this is Whatsapp number_ 09133596443_ Only Whatsapp number Don't call me just send me your message Thanks

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button