Yaushe ne wa’adin mika sunayen yan takara a Najeriya zai cika?
Yaushe ne wa'adin mika sunayen yan takara a Najeriya zai cika?

Yaushe ne wa’adin mika sunayen yan takara a Najeriya zai cika?
Daga ranar Juma’a 10 ga watan Yunin 2022 ne Hukumar Zaben Najeriya INEC ta bude kofar aike wa da sunayen Ζ΄an takarar jam’iyyuhar zuwa ranar 15 ga watan Yuli mai kamawa.
INEC ta tsara cewa za a fara gabatar da sunayen Ζ΄an takarar shugaban kasa da kuma Ζ΄an majalisun tarayya daga ranar 10 ga watan Yuni har zuwa ranar 17 ga watan na Yuni.
Sai kuma sunayen Ζ΄an takarar gwamna da Ζ΄an majalisun jihohi da za a fara miΖawa daga ranar 1 ga watan Yuli zuwa 15 ga watan na Yuli.
INEC ta sanar a shafinta na Tuwita a ranar Laraba cewa “Dole a Ιora duka sunayen Ζ΄an takara a kan intanet Ιin hukuma kafin wa’adin ya cika.”
Dalilan da ke sa ‘yan siyasar Najeriya suke sauya sheka a siyasa
Zaben fitar da gwani na APC: Labaran Ζarya da aka yaΙa a kansa
Mai magana da yawun hukumar ta INEC Zainab Aminu Abubakar ta ce hukumar ta ja kunnen jam’iyyun da su kiyaye dokokin da aka shata wurin tsayar da Ζ΄an takara don gudun abinda zai je ya dawo.
“Muna sa ran cewa jam’iyyun siyasa su tabbatar da cewa sunayen da za su aike wa hukumar zabe ya zama wadannan sunayen sun samu ne a hanyar yin tsabtatattun zaΙuka na cikin gida.,” in ji Zainab Aminu.
Ta kuma nanata cewa babu batun tsawaita wa’adin sunayen Ζ΄an takarar, ba kamar yadda aka yi a lokacin gudanar da zabukan fid da gwani ba.
“Muna fatan dukkan jam’iyyun siyasa su yi amfani da wannan wa’adin da aka ba su domin yin wannan aiki da ya kamata.
Ta Ζara da cewa “Kamar yadda muke nanatawa har kullum canza wani abu a jadawalin zaben, zai iya kuma canza wani abu da ke gaba, da aka tsara shi a wannan jadawalin zaben na shekara ta 2023,” in ji ta.
Yanzu haka jam’iyyu na ta tattaunawa da masu ruwa da tsaki ne don fitar da wadanda za su mara musu baya a matsayin mataimaka a babban zaben.
“Saboda karin haske, hukumar na son tuna wa jam’iyyu cewa sai yan takarar da suka yi nasara ta halastacciyar hanyar da aka aminta da ita wurin zaben fid da gwani, kamar yadda yake kunshe a sashe na 84 na dokar zaben 2022 aka yadda a mika sunayen su.”
“Kazalika sunayen yan takarar kujerar Shugaban kasa da gwamnoni za a mika sunayensu ne tare da mataimakansu, idan ba haka ba za a soke takarar baki daya,” a cewar INEC.