World News 📻

Yanzu Yanzunan Yan Bindiga Garkuwa Da Duban Mutane A Hanyar Sokota Zuwa Gusau

Yanzu Yanzunan Yan Bindiga Garkuwa Da Duban Mutane A Hanyar Sokota Zuwa Gusau

Yanzu Yanzunan Yan Bindiga Garkuwa Da Duban Mutane A Hanyar Sokota Zuwa Gusau

Wani abun bakin ciki ya sake samun Najeriya bayan an yi garkuwa da wasu yan kasuwa 50 a Gusau, jihar Zamfara

An tattaro cewa mutanen da abun ya ritsa da su san kasance yan kasuwa da ke sayar da wayoyi a wata shahararriyar kasuwar wayoyi ta Bebeji Plaza

Sai dai kuma, rundunar ‘yan sandan jihar
Zamfara ta tabbatar da faruwar lamarin inda ta ce mutum 20 daga cikin 50 da aka sace sun kubuta

Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Zamfara – Wani rahoto da ke zuwa mana ya tabbatar da sace matasa akalla guda 50 a hanyar Sokoto-Gusau a ranar Asabar, 11 ga watan Yuni.

An kuma tattaro cewa lamarin ya afku ne da yamma yayin da mutanen da aka sace ke a hanyarsu ta komawa Sokoto inda suka halarci daurin auren daya daga cikin abokan sana’arsu.

Wani ganau ya ba da labarin lamarin

Da yake tabbatar da lamarin ga wakilin Legit.ng daraktan hulda da jama’a na kungiyar yan kasuwar Bebeji Plaza, Zulkifilu Muhammad wadanda lamarin ya ritsa da su suna tafiya a motocin basu uku lokacin da masu garkuwa da mutanen suka kama su a kusa da garin Tureta hanyar Sokoto/Zamfara, iyakar jihohin biyu.

Wani mai suna Usman ya fada ma Legit.ng cewa ya shiga dimuwa kan lamarin yayin da yake kuma rokon gwamnatin jihar Zamfara da hukumomin tsaro da su dauki matakan gaggawa don ceto wadanda aka sace cikin gaggawa.

A halin da ake ciki, rundunar yan sandan jihar Zamfara ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce an saki mutum 20 cikin mutanen da aka sace.

Kakakin yan sandan rundunar, SP Shehu Muhammad ya sanar da wakilin Legit.nga Zamfara cewa cikin mutum fiye da 50 da aka sace 20 sun samu yanci bayan maharan sun yi watsi da su a hanya.

Ya ce rundunar ta tura tawagar bincike da ceto zuwa yankin domin su ceto sauran mutanen.

masu sauraranmu a koda yaushe bayan kun karanta wannan labarin zamu so karben ra’ayoyimku a sahen mu na tsokaci.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button