Political News 🌐

Yanzu-Yanzu: Shugaban majalisa ya fice daga APC ya koma jam’iyyar PDP

Yanzu-Yanzu: Shugaban majalisa ya fice daga APC ya koma jam'iyyar PDP

Yanzu-Yanzu: Shugaban majalisa ya fice daga APC ya koma jam’iyyar PDP

Shugaban majalisar dattawa, Sanata Yahaya Abdullahi ya sauya sheka daga jam’iyyar APC zuwa jam’iyyar adawa ta PDP a jihar Kebbi, inji Punch.

Mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Muhammad Jamil Gulma, wanda ya tabbatar da sauya shekar ya ce: “Shugaban majalisar dattawa, Dakta Yahaya Abdullahi a ranar Laraba da karfe 9 na safe zai bar Abuja zuwa Kebbi, ya zarce karamar hukumar Kamba domin shelanta shiga jam’iyyar PDP, kuma zai nuna sha’awar sa ta tsayawa takarar kujerar a yanzu.”

Dokta Yahaya wanda ya halarci zaben fidda gwani na gwamnan jihar Kebbi na jam’iyyar APC bai samu kuri’a ko daya ba, sakamakon da ya ki amincewa da s
hi kuma ya bayyana shi a matsayin wasan kwaikwayo kuma wasan yara

Masu fashin baki dai sun ce ficewar tasa ba za ta rasa nasaba da zaben fidda gwanin takarar gwamnan da wasu da dama a shugabannin jam’iyyar APC mai mulki suka yi masa makarkashiya ba.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button