Political News 🌐

Yanzu yanzu atiku Abubakar ya taya Bola Tinubu murnar lashe tikitim APC

Yanzu yanzu atiku Abubakar ya taya Bola Tinubu murnar lashe tikitim APC

Yanzu yanzu atiku Abubakar ya taya Bola Tinubu murnar lashe tikitim APC

Abuja – Ɗan takarar shugaban ƙasa da jam’iyyar PDP ta tsayar, Alhaji Atiku Abubakar, ya taya jagoran APC na ƙasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, murnar samun nasara.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasan ya ta ya Tinubu murnan ne a wani rubutu da ya yi shafinsa na dandanlin sada zumunta Tuwita. Tinubu, ya lashe zaɓen fidda ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC bayan shafe kwanaki ana gudanar da babban taron APC na musamman a Abuja.

Da yake taya jagoran APC na ƙasa murna, Atiku ya ce bayan dogon lokaci ana fafatawa daga ƙarshi jajircewar ɗan takaran ce ta rinjaya.

Atiku Abubakar ya ce

Ina taya murna ga Bola Tinubu @OfficialABAT bisa zama ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyarka. Bayan shafe lokacin ana fafata wa, amma daga ƙarshe jajircewarka ce ta rinjaya

 

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button