Political News 🌐

Yantakara uku sun janye wa mataimakin shugaban ƙasa yemi osinbajo

Yantakara uku sun janye wa mataimakin shugaban ƙasa yemi osinbajo

Yantakara uku sun janye wa mataimakin shugaban ƙasa yemi osinbajo

Daraktan kamfen na mataimakin shugaban kasa, Sanata Kabiru Gaya, ya ce wasu yan takara uku sun janye wa Osinbajo

Sanatan ya ce a halin yanzun sauran yan takara biyu kacal suka rage, Bola Ahmed Tinubu da Farfesa Yemi Osinbajo

A halin yanzun komai ya kankama a wurin taro bayan hallaran manyan mutane ana dakon fara kaɗa kuri’a
Abuja – Daraktan Kamfen na mataimakin shugaban kasa, Sanata Kabiru Gaya, ya ce yan takarar shugaban ƙasa a APC sun ragu zuwa mutum biyu, Farfesa Yemi Osinbajo da Bola Tinubu.

Punch ta rahoto Gaya na cewa yan takara guda uku daga ciki masu neman gaje Buhari sun janye wa mataimakin shugaban ƙasa,
Sanata Gaya mai wakiltar mazaɓar Kano ta kudu a majalisar datttawa, ya shaida wa Channels tv cewa masu neman kujerar shugaban ƙasa sun koma mutum biyu.

Sanata Gaya yace
Yanzu muna da mataimakin shugaban ƙasa, Yemi Osimbajo, da Bola Ahmed Tinubu. Na samu labarin yan takara uku sun janye wa Osimbajo, Nnamani da wasu biyu sun janye wa Osinbajo.

” Duk da jaridar ta gaza tabbatar da ikirarin sanatan, amma dai Nnamani ya sanar da janyewa daga takarar, inda ya bayyana hakan da siyasar yankin kudu maso gabas. Kungiyar gwamnonin arewa sun miƙa wa shugaban ƙasa Buhari jerin yan takara 5 da suka ganin sun fi dacewa APC ta ba ɗaya tikitin takara
Daga cakin yan takaran har da mataimakin shugaban kasa, Farfesa Osinbajo da kuma jagoran APC na ƙasa Bola Ahmed Tinubu.

Anfarataro bayan zuwan shugabankasa buhari
Bayanai sun bayyana cewa tuni kamai ya kankama ka’in da na’in tun bayan isar shugaba Buhari filin Eangle Square, Uwar gidansa, Hajiya Aisha Muhammadu Buhari, ta isa filin.

 

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button