Political News 🌐

Yan APC da suka yi nasara, da ‘yan biyu-babu da wadanda su ka fi shan kunya a zaben gwani

Yan APC da suka yi nasara, da 'yan biyu-babu da wadanda su ka fi shan kunya a zaben gwani

Yan APC da suka yi nasara, da ‘yan biyu-babu da wadanda su ka fi shan kunya a zaben gwani

Nasarar Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a zaben fitar da gwani zai canza yadda siyasar APC ke tafiya

Akwai masu neman takarar da suka gyara alakarsu da Bola Tinubu a zaben tsaida β€˜dan takaran

Wasu kuma sun sha kashi a zaben, ana tunani fito-na-fiton da suka yi ya nakasa su kenan a siyasa
Abuja – Jaridar Premium Times ta fitar da rahoto a game da wadanda suka samu galaba da wadanda suka samu akasin haka a zaben fitar da gwanin APC.

Wadanda suka yi nasara

1. Bola Tinubu Babban wanda ya yi nasara a zaben shi ne Bola Tinubu wanda ya samu tikiti da kuri’a 1271. Tinubu ya dade yana aiki domin ganin zuwan wannan ranar.
2. Gwamnonin Arewa Wasu rukunin da zaben ya yi masu kyau su ne gwamnonin Arewa da suka dage a kan mikawa β€˜dan kudu takara, kuma da-damansu suka samu yadda suke so.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar 3. Kayode Fayemi A dalilin janye takararsa da ya yi, Kayode Fayemi ya gyara alakarsa da Bola Tinubu. Ana yi masa zargin ya ci amanar tsohon Ubangidansa, yanzu ya wanke kansa. 4. Godswill Akpabio da sauransu Ministan Neja-Delta shi ne ya fara bude kofar janye takararsa. Jaridar ta ce hakan zai taimakawa siyasar Godswill Akpabio da duk sauran wadanda suka bi sahunsa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button