World News 📻

Turkashi’Yan bindiga sun sace shugaban matasa, sun haɗa da Motoci maƙare da kuɗi a Sakatariya

Turkashi'Yan bindiga sun sace shugaban matasa, sun haɗa da Motoci maƙare da kuɗi a Sakatariya

Turkashi’Yan bindiga sun sace shugaban matasa, sun haɗa da Motoci maƙare da kuɗi a Sakatariya

Wasu miyagun yan bindiga sun kai samame Sakatariyar ƙaramar hukumar Ihiala ta jihar Anambra sun aikata babbar ɓarna

Bayanai sun nuna cewa maharan sun sace shugaban matasan yankin, yayin da suka haɗa da Motoci masu tsada

Kakakin hukumar yan sanda reshen jihar Anambra ya ce har yanzun ba su samu rahoton faruwar lamarin ba .

Anambra – Yan bindiga sun yi awon gaba da wani shugaban matasa a ƙaramar hukumar Ihialia da ke jihar Anambra, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Wata majiya a yankin ta bayyana cewa bayan sace shugaban matasan, maharan sun kai samame Sakatariyar ƙaramar hukuma suka kwashi motoci masu darajar miliyoyin kuɗi da aka tanada son tallafawa mutane.
Shugaban ƙungiyar cigaban matasa ta Okija, Kwamaret Ononuju Maxwell Chigozie, a wata sanarwa ya ce mazauna yankin sun shiga ƙunci sanadiyyar harin.
A cewarsa, Honorabul Chuddy Ifeanyi Momah, shi ya aje motocin da maharan suka sace da nufin rabawa mutanen mazaɓar ƙaramar hukumar Ihiala.
Ya ƙara da cewa ɗan majalisar tarayyan ya aje motocin ne yana jiran lokacin da ya dace ya rabawa mutanen mazaɓarsa da niyyar taimaka musu kafin lamarin ya faru.

A jawabinsa shugaban ƙungiyar matasan ya ce: “Maganar gaskiya mummunan lamarin ya auku ne da tsakar dare, a lokacin suka tasa shugaban matasan mu, suka tilasta masa ya nuna musu inda aka aje motocin waɗan da sun kai darajar miliyan N50m.”

 

 

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button