Political News 🌐

Tofa Daga Karshe Akwai Yiyuwar Bola Ahmad Tinubu Zai Janye Daga Takarar Shugaban Kasa A Jam’iyyar Apc

Tofa Daga Karshe Akwai Yiyuwar Bola Ahmad Tinubu Zai Janye Daga Takarar Shugaban Kasa A Jam’iyyar Apc

Tofa Daga Karshe Akwai Yiyuwar Bola Ahmad Tinubu Zai Janye Daga Takarar Shugaban Kasa A Jam’iyyar Apc

Wani labari da ya riskemu a yanzu shine ta yadda aka bayyana akwai yiyuwar bola ahmad tinubu zai janye daga neman takarar shugaban kasa kan dalilin matsi da yake fuskanta daga jam’iyyar apc kamar yadda shafi daily news hausa suka wallafa

DA DUMI-DUMINSA: Akwai Yiyuwar Bola
Ahmad Tinubu, Ya Janye Takaran Sa Na Tsawa Shugaban Kasa

Jagoran jam iyyar APC na kasa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu na fuskantar matsin lamba a Jamiyyar APC a halin yanzu.

Ya kamata Bola Ahmad Tinubu ya hakura da aniyarsa ta zama shugaban kasa Kamar Yadda Wata majiya ta jam’iyyar ta bayyana a safiyar yau.

Ta kara da cewa a makon da ya gabata ne
shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tura wasu shugabannin jam iyyar domin shawo kan Tinubu ya hakura.

An tattaro cewa babban mai neman takarar ya fusata da sakon inda ya shaida wa wakilan shugaban kasa dalilin da ya sa zai tura sua lokacin da zai iya kiransa ko ya gayyace shi don tattaunawa.

Tinubu yace a isar masa da sakon idan har
shugaba Buhari yana da dalilin da zai hana ya goya masa tikitin takara babu laifi shugaban ya kira shi ya tattauna a kai maimakon ya yi ta zagaye-zagaye domin hana shi dama,” inji majiyar.

Sai dai kuma ance shugaban kasa da wasu
mutanen da ke kusa da shi watakila sun fusata Tinubu yayin ganawarsa da wakilan jam’iyyar a Abeokuta Jihar Ogun a ranar Alhamis din da ta gabata.

An gano cewa taron shugabannin jam’iyyar da suka kira a Abuja da yammacin ranar Asabar ya kasa shawo kan Tinubu ya sauka daga mulki ko da an ce akwai shirye-shiryen samar masa da sauki saboda matsayinsa na shugaban jamiyyar na kasa, wata majiya mai tushe ta ce.

masu sauraranmu a koda yaushe bayan kun karanta wannan labarin zamu so karben ra’ayoyinku a sahen mu na tsokaci sannan idan wannan ne karanka na farko da ka dana mana alamar kararrawar sanarwa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button