Political News 🌐

Talaka ba zai shiga aljanna ba saboda yawan korafinsa, Minista

Talaka ba zai shiga aljanna ba saboda yawan korafinsa, Minista

Talaka ba zai shiga aljanna ba saboda yawan korafinsa, Minista

Ministan harkokin cikin gida na kasar Uganda, Mista Kahinda Otafire, ya bayyana cewa talakawa ba za su shiga aljanna ba Ya sanar da cewa, yawan korafin da talaka ke kaiwa Ubangiji da koke a kowacce rana ne yasa ba za a shigar da shi aljanna ba Ya yi kira ga dalibai da su mike su nemi kudi tun da karfinsu a maimakon su yi ta kai koke da korafe-korafe

Mista Kahinda Otafire, ministan harkokin cikin gida na kasar Uganda, ya fada wani hali bayan ya furta wasu kalamai da ke

nuna cewa talaka ba zai shiga aljanna ba. Ministan ya ce, talaka ba zai shiga aljanna ba saboda suka da yake yi Ubangiji wurin mika kokensa a kowacce rana, Aminiya Daily Trust ta ruwaito.

Ministan a lokacin jawabin da ya yi yayin wani taron dalibai a Kyenjojo, ya sanar musu da cewa kada su zargi Ubangiji idan sun gaza amfani da damar da ya basu na yakar takaici inda ya shawarce su da su dage wurin neman arziki a madadin korafin da suke yi a kowacce rana

Ministan ya kara da cewa, halayyar sukar Ubangiji da talakawa ke yi ita za ta hana su shiga aljanna
Babu shakka wannan lamarin ya janyo cece-kuce inda wasu Malaman addinai da kungiyoyi suke zargin gwamnati da gazawa wurin samar da yanayi mai kyau da har talakawa za su samu sassauci daga halin matsin da suke ciki

 

 

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button