SIYASAR JIHAR TARABA DA BANBANCIN ADDINI
SIYASAR JIHAR TARABA DA BANBANCIN ADDINI

Babu shakka jihar Taraba Musulmai su ke da rinjaye, amma wadanda ba Musulmai ba suke shugabancin jihar, suna tauye hakkin Musulunci da Musulmai ta kowani bangare
Akwai manyan mutane masu tasiri a Kasarnan ‘yan jihar Taraba irinsu Theophilus Yakubu Danjuma wanda yayi alwashin cewa muddin yana raye Musulmi ba zai mulki jihar Taraba ba
Gwamnan Jihar Taraba na yanzu Darisu Ishaku ba Musulmi bane, yana jam’iyyar PDP, kuma wannan shine wa’adin mulkinsa na karshe, da akayi zaben fitar da gwani sun zabi wani tsohon soja wanda ba Musulmi ba domin ya yi takaran Gwamna
A bangaren jam’iyyar APC na jihar Taraba, kusan za’a ce Musulmi sun karkata zuwa ga jam’iyyar domin su tsayar da dan takara Musulmi Professor Muhammad Sani Yahaya, hakanan suka hadu suka reni jam’iyyar suka mata hidima
Amma da akazo zaben fitar da Gwani, sai manyan ‘yan siyasar jihar Taraba wadanda ba Musulmai ba suka hada baki da baragurbin Musulmai ‘yan jam’iyyar APC aka saye Daliget da makudan kudade sukayi watsi da dan uwansu Musulmi Professor Muhammad Sani suka zabo wanda ba Musulmi ba Emmanuel Bwacha
Wannan ne dalilin da yasa Professor Muhammad Sani da magoya bayansa suka fice daga jam’iyyar APC suka koma NNPP, kuma aka bashi takaran Gwamna
Abune tabbatacce babu yadda za’ai a samu nasara akan Musulmai sai idan Musulman sun kauce hanyar Allah sannan basu hada kai ba, rashin hadin kai ga Musulmin jihar Taraba shi ya jawo ake musu mulkin mallaka tare da tauye musu hakkinsu
Don haka muna kira ga ‘yan uwa Musulmin jihar Taraba, kuyi watsi da jam’iyyar PDP da APC kuzo ku goyi bayan ‘dan uwanku Musulmi a NNPP, domin ya ‘yantoku daga danniya da zalunci da wariya da mulkin mallaka da ake muku a Taraba, kanku zaku yiwa ba wani ba
Muna rokon Allah Ya tabbatar wa Musulunci da Musulmai nasara a jihar Taraba