World News 📻

Masoyana kutayani murnar karin,aure taredasamun zaman lafiya wannan shine video nadaurin auren jarumi Adam Zango da jaruma aisha humaira

Masoyana kutayani murnar karin,aure taredasamun zaman lafiya wannan shine video nadaurin auren jarumi Adam Zango da jaruma aisha humaira

Masoyana kutayani murnar karin,aure taredasamun zaman lafiya wannan shine video nadaurin auren jarumi Adam Zango da jaruma aisha humaira

Fitaccen dan wasa kuma mawakin Hausa, Adam A. Zango ya yi murnar cikarsu shekaru uku da sahibarsa, Safiya Chalawa Zango ya nuna farin ciki cewa duk da tarin kalubalen da suka fuskanta a rayuwar aurensu, ga shi tafiya ta fara mika

Ya kuma saki wasu zafafan hotunansu a shafinsa na soshiyal midiya, inda ya rubuta wasu zantuka masu ratsa zuciya

A ranar Alhamis, 26 ga watan Mayu ne shahararren dan wasan nan na Hausa kuma mawakin zamani, Adam A. Zango ya cika shekaru da auren amaryarsa, Safiya Chalawa. Adam Zango ya raya wannan rana ta musamman inda ya saki wasu zafafan hotunansa da matar tasa domin murnar wannan tafiya da ta fara mika a rayuwarsu.

Ana ganin wannan murna tasa ba zai rasa nasaba da yadda suka shafe tsawon shekaru uku ba tare da an ji kansu da amaryar tasa ba sakamakon lakabi da ake masa da mai yawan auri-saki.

Mawakin ya kuma nuna godiya ga Allah a kan yadda suka iya kaiwa war haka duk da tarin kalubale da suka dunga fuskanta tun daga ranar da aure ya kullu a tsakaninsu.

Ya rubuta a shafinsa na Instagram:

“Ma shaa Allah, aurenmu ya cika shekaru uku a yau! Ina matukar farin ciki da ganin cewa mun tsallake duk wasu kalubale da suka tunkare mu tun daga ranar da nace: “Eh na yarda”. Sai an daure an kuma yi hakuri sannan ake samun farin ciki a tsakanin ma’aurata. Ina fatan za mu ci gaba da rike soyayyar da hakuri wacce ta haifar da wannan aure mai cike da farin ciki yayin da muke ci gaba da rayuwa a tare. Ina tayamu murnar zagayowar shekara

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button