Political News 🌐

Magoya bayan Tinubu sun fara murna tun kafin gama zaɓe

Magoya bayan Tinubu sun fara murna tun kafin gama zaɓe

Magoya bayan Tinubu sun fara murna tun kafin gama zaɓe

Abin da shugaba Buhari ya faɗa wa Deleget a wurin taron APC kafin fara zaɓe

Legit.ng na ta kawo muku yadda zaben ke gudana kai tsaye daga filin wasa na Eagle Square da ke babban birnin tarayya na Abuja.

An fara shirin tantance kuri’un da aka kada

A yanzu haka, ana shirin tantance kuri’un da deliget suka kada domin sanar da wanda ya yi nasarar lashe zaben fidda gwanin na APC.

An gano wakilan zabe dauke da akwatunan kuri’un da aka kada yayin da dandanzon jama’a da jami’an tsaro suka sanya su a tsakiya.

Yanzu Yanzu: An gama kada kuri,a

An kammala kada kuri’a a babban zaben fidda gwanin shugaban kasa na jam’iyyar APC.
Zaben, wanda aka fara da misalin karfe 2:00 na tsakar dare, ya zo karshe da karfe 7.45 na safiyar Laraba kamar yadda jaridar Daily Trust ta rahoto.

Magoya bayan Tinubu sun fara murna tun kafin gama zaɓe

Magoya bayan jagoran APC na kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, sun fara tiƙa rawa a filin taron yayin Deleget ke cigaba da kaɗa kuri’u a Eagle Square.

Deleget na cigaba da kaɗa kuri,u

Barkan mu da safiya, Legit.ng zata cigaba da kawo mutu abubuwan da ke wakana daga Filin taron APC na zaɓen fitar da ɗan takarar shugaban ƙasa, tuni dai wakilai suƙa fara kaɗa kuri’un su.

Zuwa yanzun Deleget na jihohi kusan 30 sun kammala kaɗa kuri’un su, ana tsammanin kammala zaɓen nan ba da jimawa ba, bayan haka tantancewa da ƙirga kuri’u zai biyo baya.

 

 

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button