Shafin_Wasanni ⚽🏂🚴🪂
Trending

Kasuwar ƴan ƙwallo: Makomar Saka, Tchouameni, Rashford, Eriksen, Nunez

Kasuwar ƴan ƙwallo: Makomar Saka, Tchouameni, Rashford, Eriksen, Nunez

Manchester City ta musanta cewa tana sha’awar daukar Bukayo Saka, dan wasan gaba na Arsenal mai shekara 20. (Mirror)

Real Madrid da Aurelien Tchouameni sun amince kan euro miliyan 100 domin dan wasan kungiyar Monaco da Faransa mai shekara 22 ya koma kungiyar. (Athletic)

Tottenham ta fara tattaunawa da Manchester United kan Marcus Rashford, dan wasan gaba na Ingila mai shekara 24 ko ya koma arewacin Landan da buga tamaula. (Caught Offside)

West Ham ta tura jami’anta su kalli yadda Christian Eriksen, dan wasan tsakiya dan kasar Denmark da Brentford mai shekara 30 ke taka leda. Akwai yiwuwar kungiyar ta dauki abokinsa Joakim Maehle, dan wasa mai shekara 25. (Star)

Salah ya yi amai ya lashe, Chelsea za ta dauki Matthijs de Ligt
Neymar ya kusan tarar da Pele a yawan ci wa Brazil kwallaye
Lewandowski ya lashe takalmin zinare a nahiyar Turai karo biyu a jere
Manchester United da Newcastle na cikin kungiyoyi biyu da ke daf da daukan Darwin Nunez, dan wasan Benfica da Uruguay mai shekara 22. (Sebastian Giovanelli via Star)

Kocin Chelsea Thomas Tuchel ya sami tabbaci daga wanda ya sayi kungiyar wato Todd Boehly cewa zai sami damar sayo sababbin ‘yan wasa domin iya tunkarar kungiyoyi kamar Liverpool da Manchester City a kakar wasa mai zuwa. (Telegraph – subscription required)

Aston Villa ba ta sha’awar daukan Yves Bissouma, dan wasan tsakiya na Brighton da kasar Mali mai shekara 25. (Athletic)

Dan wasan gaba na Poland Robert Lewandowski, mai shekara 33, ya ce zai bar Bayern Munich saboda yana bukatar sauyi a rayuwarsa, kuma ya ce “kungiyar tasa ba ta son sauraronsa.” (Bild – in German)

Ga Bidiyon sai kukala 👇👇👇👇👇

 

By C.E.O Founder OF Mr ATG News Auwal Telan Gayu

Hello my Fallowers My Name is_Real_Auwal_Telan Gayu_ C.E.O_Founder OF_MR ATG News.com_my followers this is Whatsapp number_ 09133596443_ Only Whatsapp number Don't call me just send me your message Thanks

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button