Political News 🌐

Kai Tsaye: Yadda ake Gudanar da Zaɓen Fidda Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa na APC

Kai Tsaye: Yadda ake Gudanar da Zaɓen Fidda Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa na APC

Kai Tsaye: Yadda ake Gudanar da Zaɓen Fidda Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa na APC

Muna ta kawo muku yadda zaben ke gudana kai tsaye daga filin wasa na Eagle Square da ke babban birnin tarayya na Abuja

An fara shirin tantance kuri’un da aka kada

A yanzu haka, ana shirin tantance kuri’un da deliget suka kada domin sanar da wanda ya yi nasarar lashe zaben fidda gwanin na APC.

An gano wakilan zabe dauke da akwatunan kuri’un da aka kada yayin da dandanzon jama’a da jami’an tsaro suka sanya su a tsakiya.

Yanzu Yanzu: An gama kada kuri’a

An kammala kada kuri’a a babban zaben fidda gwanin shugaban kasa na jam’iyyar APC. Zaben, wanda aka fara da misalin karfe 2:00 na tsakar dare, ya zo karshe da karfe 7.45 na safiyar Laraba kamar yadda jaridar mu takesamun labarai kaiysaye

Dukkan deliget ddin ihohi 35 da na FCT sun kada kuri’unsu, deliget din jihar Akwa Ibom ne kadai ba su yi zabe ba sakamakon umarnin kotu.

Magoya bayan Tinubu sun fara murna tun kafin gama zaɓe,

Magoya bayan jagoran APC na kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, sun fara tiƙa rawa a filin taron yayin Deleget ke cigaba da kaɗa kuri’u a Eagle Square.

Zuwa yanzun Deleget na jihohi kusan 30 sun kammala kaɗa kuri’un su, ana tsammanin kammala zaɓen nan ba da jimawa ba, bayan haka tantancewa da ƙirga kuri’u zai biyo baya.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button