Political News 🌐

Jaruma Minal na shan caccaka kan zarginta da kashe auren Maimunatu da Ado Gwanja

Jaruma Minal na shan caccaka kan zarginta da kashe auren Maimunatu da Ado Gwanja

Jaruma Minal na shan caccaka kan zarginta da kashe auren Maimunatu da Ado Gwanja

Jarumar Minal Ahmad wacce aka fi sani da Nana Izzar so tana ci gaba da shan caccakar akan zargin kashe auren Ado Gwanja da Maimunatu, Tashar Tsakar Gida ta ruwaito.

Wannan ya biyo bayan hawa sabuwar wakarsa da ta yi mai suna Warrrr a ranar Juma’a tana kwasar rawa, hakan ya tunzura mabiyanta su ka hau caccakarta.

Jaruma Minal na shan caccaka kan zarginta da kashe auren Maimunatu da Ado Gwanja

Wannan ya samo asali ne daga wani bidiyo da Murja TikTok ta yi wanda ta yi shagube akan wata da ake zargin Minal ce, inda Munat Gwanja ta yi tsokaci tana zarginta da kashe mata aure.

Daga nan ne mutane su ka gamsu da cewa akwai hannun Minal din a batun mutuwar auren Gwanjan.

Masu tsokacin sun hada da Nigerian wacce ta ce:

Yayin da mutane su ke ta tururuwar yin aikin Ummara a watan Ramadana, Labarun Hausa ta gano yadda mawaki Ado Gwanja da tsohuwar matarsa, Maimunatu suka tafi Saudiyya.

Sai dai alamu suna nuna cewa tafiyar kowa daban don yayin da suka sanya hotunansu a kafafen sada zumuntar zamani ta Instagram, kowa daban.

Β Sai dai alamu suna nuna cewa tafiyar kowa daban don yayin da suka sanya hotunansu a kafafen sada zumuntar zamani ta Instagram, kowa daban.

Maimunatu ta sanya hotunanta tare da wata yayin da Ado Gwanja ya sanya hotonsa shi kadai.

Tun a cikin jirgin sama Maimunatu ta fara daukar hotuna har lokacin da ta isa kasa mai tsarki.

Wannan kadai ya kara tabbatar da zargin mutuwar aurensu da mutane suka dinga yi kwanakin baya domin da suna da aure da tare za su tafi kuma su dauki hotuna tare.

Muna fatan Ubangiji ya daidaitasu ko kuma ya yi wa kowa zabi mafi alkhairi.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

 

 

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button