El,rufa,i zulum,boss,da yansiyasar siyasan Arewa 8 da a cikinsu za a nemi Mataimakin Tinubu
El,rufa,i zulum,boss,da yansiyasar siyasan Arewa 8 da a cikinsu za a nemi Mataimakin Tinubu

El,rufa,i zulum,boss,da yansiyasar siyasan Arewa 8 da a cikinsu za a nemi Mataimakin Tinubu
Abin da ya ragewa jamβiyyar APC shi ne fito da βdan takarar kujerar mataimakin shugaban kasa
Ciwon kan Asiwaju Bola Tinubu bayan lashe tikitin APC shi ne zaben wanda zai nemi mataimaki
Ana tunanin Bola Tinubu zai dauko abokin takararsa ne daga cikin gwamnonin jihohi masu-ci a yau
Gajerin sunannasu kamar haka
1. Atiku Abubakar Bagudu
Na farko a jerin
shi ne Sanata Atiku Abubakar Bagudu. Gwamnan Kebbi shi yake rike da kujerar shugaban gwamnonin APC na kasa, don haka yake dama.
2. Nasir El-Rufai
Ana kawo Gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai a wannan jeri. Gwamnan ya tsaya tsayin-daka wajen ganin an ba βYan kudu takara a zabe mai zuwa.
3. Abdulahi Umar Ganduje
Daga cikin wadanda suka dade su na goyon bayan Bola Tinubu akwai Abdullahi Umar Ganduje. Hakan zai iya murkushe karfin Kwankwasiyya a jihar Kano.
4. Simon Bako Lalong Gwamnan Filato,
Simon Bako Lalong zai iya dacewa da wannan kujera. Sai dai ya goyi bayan Rotimi Amaechi ne a zaben APC, amma zai jawo kuriβun kiristoci.
5. Boss Mustapha
Wani Kiristan da zai iya kwadaito kuriβun wadanda ba Musulmai ba shi ne Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, ya fito ne daga Arewa maso yamma
6. Kashim Ibrahim-Imam
ya hada da Kashim Ibrahim-Imam wanda ya yi wa PDP takarar gwamna a Borno. Imam yana cikin mafi kusanci da βdan takaran na APC
7. Abubakar Badaru
Shi ma Gwamnan Jigawa, Muhammadu Badaru Abubakar yana da karfi a jamβiyyar APC, har ya yi yunkurin ya nemi takara, daga baya sai janyewa Bola Tinubu.
8. Babagana Zulum
Farfesa Babagana Umara Zulum shi ne na karshe a jerin na mu. Gwamnan na Borno yana da farin jini a Najeriya, amma ya nuna bai shaβawar shiga siyasar kasa.
ya nuna Asiwaju Bola Tinubu zai yi zama da Gwamnonin APC nan ba da dadewa ba domin tsaida abokin takararsa a zabe mai zuwa. Babu mamaki kungiyar PGF ta gwamnonin APC
ta taka rawar gani wajen dauko wani daga Arewa maso yamma ko maso gabas a tikitin jam’iyyar mai mulki.
CEDARJUICECOM