World News 📻
Trending

An sace ƴan kasuwa ‘kusan 40’ a hanyar Sokoto zuwa Zamfara

An sace ƴan kasuwa 'kusan 40' a hanyar Sokoto zuwa Zamfara

Wasu da ake zargin ƴan bindiga ne sun sace kusan mutum 40 a hanyar zuwa Jihar Zamfara daga Sokoto.

Jama’ar da aka sace akasarinsu masu sana’ar sayar da wayoyin sadarwa ne a kasuwar Bebeji Plaza da ke Jihar Zamfara. Rahotanni sun ce sama da mutum 60 ne ƴan bindigar suka tare a hanyar, amma sama da 20 sun samu sun kuɓuta.

Shugaban kasuwar ya tabbatar wa BBC da faruwar lamarin inda ya ce an yi garkuwa da ƴan kasuwar ne a hanyar su ta dawowa daga ɗaurin auren da suka je Sokoto.

Ya bayyana cewa ƴan kasuwar sun tafi ne a cikin mota ƙirar kwasta mai ɗaukar mutum 40 da kuma mota ƙirar bas mai ɗaukar mutum 18.

Yadda rikici tsakanin Bello Turji da abokan gabarsa ya jawo mutuwar ‘yan bindiga da dama a Jihar Zamfara
Yadda ƴan bindiga suka kashe hakimi suka tayar da gari a Zamfara
A cewarsa, an sace su ne da yammacin Asabar a tsakanin Tureta da Bakura bayan sun baro ɗaurin auren da suka je a garin Tambuwal.

BBC dai ta tuntuɓi rundunar ƴan sandan Najeriya reshen Jihar Zamfara domin jin ƙarin bayani kan wannan lamari, amma ba a samu ji daga bakinsu ba.

Jihar Zamfara dai na daga cikin jihohin Najeriya da ke fama da matsalolin ƴan bindiga da masu garkuwa da mutane.

By C.E.O Founder OF Mr ATG News Auwal Telan Gayu

Hello my Fallowers My Name is_Real_Auwal_Telan Gayu_ C.E.O_Founder OF_MR ATG News.com_my followers this is Whatsapp number_ 09133596443_ Only Whatsapp number Don't call me just send me your message Thanks

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button