Shafin_Wasanni β½ππ΄πͺ
Alexandre Lacazette: Dan wasan Arsenal ya sake koma wa Lyon
Alexandre Lacazette: Dan wasan Arsenal ya sake koma wa Lyon

Alexandre Lacazette: Dan wasan Arsenal ya sake koma wa Lyon
Dan kwallon Arsenal, Alexandre Lacazette ya sake koma wa Lyon, shekaru biyar bayan ya hade da Gunners a kan fan miliyan 46 da rabi.
Lacazette ya koma kungiyar ta Faransa a kan yarjejeniyar shekaru uku har zuwa watan Yunin 2025.
Dan wasan Faransa mai shekaru 31, ya zura kwallo 54 a wasa 158 da ya buga wa Arsenal, sanna kuma ya taimaka mata lashe gasar FA Cup a shekara ta 2020.
A hirarsa da tashar Canal Plus a watan Afrilu, Lacazette ya ce “suna tuntubar juna” tsakaninsa da Lyon.
Lacazette ya kasance kyaftin din Arsenal bayan da Pierre-Emerick Aubameyang, ya koma Barcelona.